4 Janairu 2022 - 13:57
​Haitham Al-Ghais Ya Zama Sabon Babban Sakataren OPEC

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta (OPEC) ta sanar da nada Haitham Al-Ghais a matsayin sabon babban sakatarenta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Al-Ghais wanda dan kasar Kuwait ne zai maye gurbin Muhammad Sanusi Barkindo, dan Najeriya wanda ya shafe kusan shekaru shida a matsayin babban sakataren kungiyar.

A watan Yuli ne mai zuwa ne wa'adin Barkindo ke kawo karshe.

Zaben nasa ya zo ne a jajibirin taron kungiyar da kawayenta na ranar Talata.

Al-Ghais zai kama aiki a watan Agusta, yayin da wa’adin Sanusi Barkindo ke kawo karshe a watan Yuli.

Farashin danyen man fetur ya karu da kashi 0.27 cikin 100 zuwa dala 78.34 kan ganga gaya gabanin taron kungiyar kasashe masu arzikin fetur na OPEC.

342/